
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta yi nasarar kama wani matashin Nijeriya mai suna Aliyu Sanusi kan shirya zanga-zangar da ke ƙalubalantar raunin shugabanci a faɗin ƙasar.
An kama matashin ne a yammacin ranar Litinin, a hanyar Sama da ke Sakkwato, babban birnin jihar.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC, Omoyele Sowere ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar Talata inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta sako matashin, yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka.
Lamarin ya auku ne bayan da DSS ta sako wani matashin mai suna Bashir Abubakar wanda aka tsare shi a Kano kan bada goyon baya ga shiryayyen zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.
Yayin da aka sako matashin, DSS ta umarci ya mayar da rigunan da ya sa aka buga domin zanga-zangar, kamar yadda lauyansa kuma tsohon abokin takarar Sowere a zaɓen 2023, Barista Harun Magashi ya bayyana.
