Tinubu ya ɓukaci majalisa ta yi kwaskwarima ga dokar ‘yan sanda da wa’adin sufeto janar

Spread the love

A ranar Talata ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar wakilai ƙudurin gyaran dokar ‘yan sanda.

Ƙudirin dai na neman yi wa wa’adin babban Sufeto Janar na ‘yan sanda gyaran fuska.

Shugaban Tinubu ya naɗa Egbetokun a matsayin Sufeton ‘yan sanda a watan Yunin 2023 na tsawon shekaru hudu. An naɗa shi tare da sabbin shugabannin tsaro.

A cewar sashe na 18 (8) na dokar ‘yan sanda ta 2020, Egbetokun, wanda aka haifa a ranar 4 ga Satumba, 1964, ana sa ran zai yi ritaya a watan Satumba na 2024, lokacin da zai cika shekaru 60 a duniya.

Taƙaddama game da wa’adin Sufeto Janar na ‘yan sanda bai fara da shugaban ‘yan sanda na yanzu ba. Magabacin Egbetokun, Usman Baba, shima ya shiga cikin wannan cece-kuce. Baba ya cika shekaru 60 a duniya a watan Maris 2023 lokacin da ya cika shekaru 35 na hidima amma ya ci gaba da zama a ofis har aka maye gurbinsa da Egbetokun.

By ukarofi