
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A cigaba da shirye-shiryen zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi a watan Agusta, Ƙungiyar matasa ta ƙasa, NYCN ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ta da su kasance cikin shiri ganin cewa kwanakin na ƙara kusantowa.
Sanarwar ta fito daga shugaban ƙungiyar, Sukubu Sara-Igbe Sukubu cikin wata takarda da ya fitar biyo bayan wani taron gaggawa da shugabannin rassan ƙungiyar na Jihohi 36 suka gudanar ta kafar Zoom a rana Alhamis inda ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda al’ummar Nijeriya ke fama da matsanancin rayuwa musamman matasa.
Cikin matsalolin da matasan ke buƙatar gwamnati ta yi gyara a kan su sun haɗa da; hauhawar farashi da rashin tsaro da kuma rashin aikin yi a cikin al’umma musamman ga matasa wanda abin ya kai halin ni-ƴasu.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa, za ta shawarci manyan masu-ruwa-da-tsaki ciki har da jami’an gwamnati da jami’an tsaro da ƙungiyoyin al’umma da kuma gidajen jaridu domin tabbatar da gamsashshen bayani game da matsalolin don magance su.
