Ya kamata a ba matatar Ɗangote dukkan goyon baya – Kwankwaso ya shawarci Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Laraba ne tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso ya yi la’akari da rashin jituwar da ke tsakanin hukumar kula da matatar man Ɗangote da hukumomin da ke kula da harkokin man fetur NMDPRA a Nijeriya

Hukumomin Nijeriya sun zargi matatar Ɗangote da fitar da gurɓataccen man fetur mara inganci, iƙirarin da kamfanin ya musanta.

Da yake mayar da martani a shafinsa na Ɗ, Kwankwaso ya ce ya kamata gwamnatin Nijeriya da ba matatar dukkanin goyon baya don bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, domin yin barazana ga matatar a cewarsa ka iya sage wa masu zuba hannun jari a ƙasar gwiwa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaɓen 2023 ya bayyana matatar Ɗangote a matsayin muhimmiyar kadara ga buƙatun makamashi da kwanciyar hankali na tattalin arzikin ƙasa.

Ya kuma jaddada mahimmancin kare kadarorin daga duk wata barazana da ka iya kawo cikas ga ayyukanta.

“Na yi farin ciki da ziyartar matatar mai ta Ɗangote, kuma na yi mamakin irin jajircewar da aka yi wajen ganin an kafa ta.

“Lokaci ya yi da za mu haɗa kan wannan kadarorin na ƙasa don ganin cewa babban aikin bai gaza ba. Ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, kuma dole ne gwamnatin Nijeriya ta fahimci hakan ta hanyar nuna gaskiya da kuma amincewa da jarin cikin gida da na waje,” inji shi.

Tun da farko ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar da Peter Obi sun bayyana damuwarsu kan yadda rikicin da ke kunno kai tsakanin masana’antun Ɗangote da wasu hukumomin gwamnati, inda suka bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuƙa.

A rubuce-rubuce daban-daban a kan shafin Ɗ, sun koka da cewa labarin da ke faruwa wanda ke lalata matatar Ɗangote zai hana muhimmancin saka hannun jari kai tsaye daga ƙetare tare da cutar da tattalin arzikin.

Sannan sun ce dole ne hukumomin gwamnati su ba da tallafi ga matatar ta Ɗangote, inda suka ƙara da cewa matatar ta na da matuƙar muhimmanci idan aka yi la’akari da muhimmiyar rawar da take takawa wajen kyautata rayuwar al’umma.

By ukarofi