
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar ƴancin al’ummar musulmi (MURIC) da cibiyar lamuran al’ummar musulmi (MPAC) sun buƙaci a ɗauki tsauraran matakai ciki har da dakatar da wani fim da ke nuna mata sanye da niƙabi ɗauke da muggan makamai suna fashi a bankuna da laifuka masu kama da haka.
Jawabin ya fito ne daga mabanbanta ofisoshi a ranar Alhamis da su ka haɗa da Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola da shugaban MPAC, Disu Kamor.
A kwanan nan ne tauraruwar masana’antar ‘Nollywood’, Nancy Isime ta yaɗa hotunan ɗaukar fim ɗin da ake shirin fito da shi a yanar gizo waɗanda su ka nuna ta sanye da riga mara hannu da wando da kuma hijabi a cikin wasu taurari da ke sanye da niƙabi.
Hotunan sun harzuƙa mutane da dama a kafar sadarwar musamman al’ummar musulmi.
Akintola ya ce, fim ɗin ya nuna matan musulmai a matsayin ƴan fashi a cikin al’umma inda ya buƙaci a gaggauta dakatar da shi da kuma rarrashin al’umma da ya yi na cewa kar su ɗauki doka a hannusu domin hukuma za ta yi abin da ya dace a kai.
A nasa jawabin, kamor ya ce sanya niƙabi acikin shirin ba daidai ba ne, yana mai cewa hakan rashin mutuntawa ne ga kimar ƴa mace musulma.
Darakta Janar na hukumar tace finafinai ta ƙasa (NFVCB), Dakta Shuaibu Husseini ya nami waɗanda ke da alaƙa da shirya fim ɗin su yi duba tare da yin gyara a kan abubuwan da aka yi koke a kan su.
