Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Wani babban manomi kuma shugaban al’umma dake garin Agyaragu a jihar Nasarawa mai suna Alhaji Usman Adamu da aka fi sani da Doya-hamsin ya bayyana rashin jin daɗinsa a madadin manoman jihar bakiɗaya game da tsarin da aka bi aka raba takin noma wa manoman jihar wadda gwamnatin jihar ta gudanar kwanan nan.
Alhaj Usman Adamu Doya-hamsin ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da rabon takin na bana inda ya bayyana cewa “Da farko dai tambaya da ka min magana ne babba kuma in ka ga gaskiya ka ɓoye Allahi ba zai barka ba.
“Rabon takin da aka yi daga na rani har na daminan nan ni mai suna Usman Adamu Doya-hamsin a jaridu da gidajen radiyo da talabijin na faɗi ra’ayi na akan manoma cewa idan taimako na gaskiya ne mun zane mutane da ya kamata in abu na manoma ne a ba su a hannunsu.
“Amma sai ya kasance faɗa daban aiwatarwa daban, don ni a matsayina na ƙaramin manomi gwamnati ta yi bakin ƙoƙarinta amma yadda aka yi rabon kwanan nan an ce kowace mazaɓa buhu ɗari-ɗari kuma shawarar da muka bayar kafin a raba shine kowace mazaɓa gwamnati ta ɗauki ɗawainiyar kai musu takin da kan ta amma yadda aka ce a riƙa haɗa mazaɓun su huɗu ko fiye da haka su haɗu a hedikwatar ƙaramar hukumarsu a raba musu wallahi bai kamata ba.
“Da ana so takin ya shiga hannun manoman na gaskiya to da ko kwamiti da aka kafa ko shi shugaban ƙaramar hukuma a ce ya raba shi a mazaɓun ne sannan kafin a fara rabon a kira sarakuna na mazaɓun da masu unguwanni na wuraran da jami’arn tsaro masu kula da haƙƙin ɗan adam su ba su kai tsaye da kusan kashi 97 cikin 100 na manoman da sun samu takin balle ma da akace gyauta ne.
“Kuma ya kamata shugabannin ƙananan hukumomin baki ɗaya suma a riƙa umurtansu su riƙa sayowa suna rarraba wa al’ummar su ire-iren takin gyauta da sauran su kasancewa yawancin su ba sa gudanar da ayyukan cigaba wa al’ummar su kamar gyarar kwalbati da asibitoti da makarantu da sauran su kwata-kwata tunda aka zabe su a kujerun a mukamin na shugabannin ƙananan hukumomin jihar,” inji shi Usman Doya-hamsin.
Gwamnatin jihar ta Nasarawa dai a kwanan nan ne ta raba takin ne kimanin buhuna dari-dari ga manoman daga mazabun duka kananan hukumomin jihar 13 inda a yanzu al’ummar da dama musamman manoma na cigaba da korafin basu samu takin ba cewa an raba wa wadanda ba ainihin manoma ne ba.
