
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan ƴar takara Kamala Haris ta yi nasara a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe bayan da shugaban Joe Biden ya ƙudiri aniyar janyewa daga tsayawa takara.
Sanarwar ta fito ne a ranar Juma’a, kwanaki kaɗan da Kamala ta shelanta tsayawarta takarar kujerar shugabancin ƙasar.
Wata ɗaukar bidiyo, ta nuna yadda Obama ya kira ta a waya, yana mai cewa shi da matarsa, Michelle suna goyon bayan ta tare yi mata alƙawarin samun gudunmawarsu ga kai wa nasararta.
‘NBC News’ ta ruwaito cewa, kasancewar Obama shi ne baƙin fata na farko da ya mulki Amurka, ya ce yana fatan Haris ta zama mace ta farko da zata jagoranci ƙasar inda ya ce ya fara bata goyon baya ne tun bayan bayyanar tsayawarta a ranar Lahadi, inji wasu mutum huɗu da ke da alaƙa da hirar tasu.
