Tinubu ya shashantar da maganar zanga-zanga, ya ce ba ita suke tsoro ba, halin da za a jefa talaka ke damun sa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa Majalisar sarakunan gargajiya ta Nijeriya cewa gwamnatinsa ba ta shakkar zanga-zanga, yana mai cewa halin da za a jefa talakawa ke damun sa.

Ƙungiyoyin matasa sun shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya da za a yi a ranar 1 ga watan Agusta wanda ake fatan ya zama sababin magance matsalolin al’umma a faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da sarakunan a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda ya ce Nijeriya ta na ƙoƙarin farfaɗowa daga halin da ta tsinci kanta, yana mai cewa asarar da za a yi wa talaka ya ke guje wa inda ya bada misali da motoci ƙirar ‘Bus’ da aka ƙona a jihar Legas wanda ya haifar da ƙarancin ababan sufuri.

Tinubu ya kuma yi tsokaci game da cigaba da aka samu a harkar tsaro inda ya ce gwamnati na ƙoƙari wajen ganin an inganta ta.

Ya ƙara da cewa, gwamanti ta ɗauki matakan bayar da tallafi ga harkar ilimi da kuma shirya tsarin bada bashi na ‘costumer credit’ domin inganta tattalin arziƙin ƙasa da kuma cinikayya.

Bugu da ƙari, ya ce gwamnati ta na cigaba da ƙoƙarin daidaita al’amuran tattalin arziƙi, yana mai cewa ƙofa a buɗe ta ke wajen tattaunawa domin cigaban ƙasa.

Kazalika, ya ƙara da cewa, akwai buƙatar bankin harkar noma ya fara aiki domin kula da matsalolin ambaliya da ta’addanci inda ya nuna muhimmancin nazarin al’amuran da su ka shafi albarkatun tattali kafin fara aiki a kan su.

By Babaji