
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Bayan da aka tsige Sanata Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa da kuma Mataimankin shugaban kwamitin daidaito, magoya baya da taron mata daga Kudancin jihar Borno su na shirin gudanar da zanga-zangar lumana a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Koken nasu yana da alaƙa da sauke Ndume daga muƙaminsa da su ka danganta halinsa na rashin yin shuru a Majlisa da kuma caccakar gwamantin Shugaba Tinubu inda suka bada misali da matsalolin yunwa da kuma rashin tsaro.
Sanata Ndume ke wakiltar ƙananan hukumomi tara a jihar Borno inda wakilan mazuɓu 101 na mazaɓarsa su ka taru a gidansa da ke Maiduguri a ranar Alhamis, domin nuna goyon bayansu gare shi.
Mai magana da yawun matan, Misis Mada Musa ta soki matakan da gwamnati ta ɗauka, ta na mai cewa an hukunta Ndume kan abin da ya kamata a ce gwamnatin ta yi gyara a kan su na halin ƙuncin rayuwa da al’umma ke ciki.
A lokacin da ya ke jawabi, Ndume ya bayyana godiyarsa ga goyon bayan nasu, yana mai kira a gare su da su kwantar da hankula tare da kiyaye doka da oda da cigaba da gudanar da harkokinsu na noma inda ya ce zai cigaba da tallafa mu su.
Ya kuma yi tsokaci game da ƙarancin albashi na Naira 70,000 da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar inda ya ce hakan ya kasa a yanayin tsanani da al’umma ke ciki.
Kazalika, ya ƙara da tsokaci game da kiraye-kiraye na cewa ya fice daga jam’iyyar APC inda ya ce zai cigaba da bada gudunmawarsa tare da zama a cikinta gami da bada goyon bayansa ga gwamnan jihar, Babagana Zulum a ƙoƙarinsa na samar da ayyukan cigaba a yankin.
