Turji ya sake jaddada ministan Tinubu cikin masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda

Spread the love

Fitaccen ɗan bindigan nan Kachalla Bello Turji ya jaddada maganarsa da yayi na cewa, Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar zamfara ya na bada gudunmuwa sosai wajen ta’addanci a Arewacin Nijeriya.

A wani faifan bidiyo, Turji ya jaddada Matawalle ya kasance yana bada taimakon kuɗi da sauran taimako ga ‘yan ta’adda a yankin Arewacin ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan da Matawallen ya ƙaryata wannan zargin da Turji yayi masa. Ya ce wannan zargin, so a ke a zubar ma Matawalle da mutunci da kuma ɓata mashi suna.

Sai dai wannan na zuwa ne a lokacin da Arewacin Nijeriya ke fama da matsanancin rashin tsaro da kuma zargin da ake cewa wasu manyan yan siyasa na da hannu a cikin ta’azzarar lamarin.

By ukarofi