Ɗaliban Nijeriya sun fara gangamin zanga-zangar matsin rayuwa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ɗaliban Jami’o’i ta Ƙasa (NAUS), Ƙungiyar Ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Ƙasa (NAPS), da Ƙungiyar Ɗaliban Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NANCES) sun bayyana shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Litinin 29 ga watan Yuli, 2024.

Zanga-zangar mai suna “Ranar Zanga-zangar Ɗaliban Nijeriya” na da nufin jawo hankalin Gwamnatin Tarayya kan irin wahalhalun da ɗaliban Nijeriya ke fuskanta a manyan makarantun gaba da sakandire a cikin matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugabannin ƙungiyoyin uku suka sanya wa hannu, ɗaliban sun bayyana takaicinsu kan yadda gwamnati ta kasa magance matsalolinsu duk da roƙon da aka yi mata.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Bayan tuntuɓar juna sosai kan yadda ɗaliban Nijeriya za su cigaba da karatu a manyan makarantu cikin lumana, mun yanke shawarar fara wata zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna kokenmu da kuma neman ɗaukar matakin gaggawa daga Gwamnatin Tarayya.”

Ɗaliban sun buƙaci gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai domin rage raɗaɗin da suke ciki, da suka haɗa da samar da isassun kuɗaɗe don ilimi, rage kuɗaɗen makaranta, da samar da ababen more rayuwa a makarantu.

Ana sa ran gudanar da zanga-zangar a manyan biranen ƙasar, tare da halartar ɗaliban manyan makarantu daban-daban.

Shugabannin ƙungiyoyin sun buƙaci ɗaukacin ɗaliban Nijeriya da su shiga zanga-zangar su bayyana ra’ayoyinsu.

“Dole ne mu tashi tsaye don neman ‘yancinmu da kyakkyawar makoma ga kanmu da kuma ƙannenmu masu tasowa,” inji su.

By ukarofi