Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya umarci Majalisar Malamai ta jihar da su zo ai aiki tare domin ci da Jihar Zamfara gaba.
Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron Majalisar Malaman wanda a ka gudanar a harabar Majalisar wadda ke cikin gidan gwamnati a ranar Talata.
Wata sanarwa daga bakin mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya jaddada irin gudunmuwar da malaman ke bayarwa wajen tafiyar da gwamnati.
Ya ƙara da cewa tabbas Majalisar Malaman ta na taka rawa sosai wajen ganin ci gaban jihar sama da shekaru 21.
Gwamnan ya jaddada wa malaman cewa ƙofar shi a buɗe take kullum musamman wajen amsar shawarwari daga bakin malaman.
“Kamar yadda ku ka sani, wannan Majalisar an ƙirƙire ta ne bisa tsarin doka tun shekarar 2003 domin ƙarfafa matsayar shari’a musulunci.
Waɗansu daga cikin shawarwarin da a ka ba gwamnan sun haɗa ba, shawara wajen naɗa Alƙali, matsalolin da suka shafi fitar da fatawa”
Daga ƙarshe gwamnan ya yaba wa malaman bisa jajircewa da kuma taimakawa gwamnati ganin a ci da Jihar Zamfara gaba.
