
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Bayan sanara da dokar ta-ɓaci a jihar Borno, gwamnati ta sauya tsarin da ta fitar a ranar Alhamis.
Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fitar ne sakamakon bayanan sirri da ta samu inda ta ke ganin hakan zai taimaka wajen dakatar da hare-haren mayaƙan Boko Haram/ISWAP la’akari da tashin bom a ƙauyen Kawuri da aka samu a ranar Laraba da kuma a wasu sassan Maiduguri, babban birnin Jihar.
Majalisar tsaro ta sanar da sauya tsarin dokar daga ƙarfe 12:00 na rana da aka saka a jiya, zuwa ƙarfe 3:00 na rana zuwa 6:00 na safe a ranakun Juma’a da Asabar, sannan bayan haka mutane sai su cigaba da harkokinsu kamar yadda aka saba.
Wata sanarwa da majalisar tsaron ta fitar, ta ce ratar sa’o’i uku da aka samu, dama ce aka bai wa al’ummar musulmi su yi sallar jumma’a.
Hakan nan, sanarwar ta buƙaci al’umma su yi sallah a yankunansu yayin da ake cigaba da sanya ido kan halin da ake ciki a faɗin jihar.
