Yadda batun zanga-zanga ke wakana a rana ta biyu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Dawowar harkoki yadda aka saba na cigaba da wakana a jihohin Sakkwato, Taraba, Adamawa da Kebbi yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.

Sai dai, a jihohin Legas da Fatakwal a Ribas da Benin a Edo, ana cigaba da gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka faro ta a jiya.

A jihar Legas, ƴan zanga-zangar sun taru a Ojota inda jami’an tsaro su ka tsaya wajen basu kariya yayin da Kwamishinan Labarai, Gbenga Omotosho ya gabatar mu su da jawabi tare da yi mu su alkawarin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin gyara ga buƙatunsu.

Haka nan, a Fatakwal, sun taru ne a Sakatariyar Tarayya yayin da Ƴan sanda su ka gabatar mu su da jawabi.

A birnin tarayya Abuja kuma, ɗaruruwan ƴan zanga-zangar ne su ka taru a Shataletalen Berger inda Ƴan sanda su ka watsa musu hayaƙi mai sanya ƙwalla da aka fi sani da barkonon tsohuwa. Daga nan, ƴan zanga-zangar su ka yi tattaki zuwa filin wasa na Moshood Abiola wanda nan ne kotu ta amince su taru.

A jihar Kaduna kuma, babu alamar ƴan zanga-zanga a cikin gari inda garin ya kasance cikin salama.

Bayan da aka fara zanga-zangar cikin lumana a jihohi 36 da Abuja a Nijeriya, an samu tarzoma, kashe-kashe da satar dukiyar al’umma a jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa da sauran su wanda hakan ya tilasta wasu gwamnonin su ka sanya dokar hana fita.

Hukumomin tsaron Ƴan sanda da DSS sun gargaɗi jagororin zanga-zangar su janye daga batun cigaba da gudanarwa. Sai dai, yayin da jagororin su ka ce za su yi kwana 10 su na yi, hukumomin sun buƙaci su sake nazari game da hakan.

By Babaji