Shugabannin tsaro sun haɗe hannu don fuskantar matsalolin tsaro

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A wani yunƙuri na nuna haɗin gwiwa don amfanin Nijeriya da al’ummarta, manyan hukumomin tsaro sun taru a hedikwatar tsaro da ke Abuja don samar da hanyoyin warware matsalolin zanga-zanga, tashin-tashina da kuma munanan shirye-shirye da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Zaman wanda Shugaban Ma’aikatan Tsaron, Janar Christopher Musa ya jagoranta, ya ƙunshi Shugabannin rundunonin sojojin ruwa da na sama, Sufeto Janar na ‘Yan sanda, shugabannin hukumomin shige da fice da na Kwastom, Darakta Janar na DSS da sauran manyan hukumomin tsaro.

A lokacin zaman, duka jami’an sun bayar da bayanan shirye-shiryen da ka iya shafar zaman lafiyar al’ummar Nijeriya tare da tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa su na cigaba da ƙoƙari wajen ganin an daƙile su don tabbatar da zaman lafiya.

Janar Musa ya yi ƙarin haske game da buƙatar nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu, girmama ƴancin ƴan ƙasa da kuma ƙoƙarinsu na ganin an kiyaye sharuɗan gudanar da atsaye.

A lokacin da ya ke jawabi, shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya jaddada ƙoƙarin rundunarsu ta kare demokraɗiyya da zaman lafiya da kuma haɗin kan ƙasa, ya na mai cewa ba za su bari ƙasar ta wargaje ba, domin su na iya ƙoƙarinsu wajen ganin a tabbatar da kiyaye doka da oda tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi.

Haka nan, Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun ya yi gargaɗin ayyukan cin amanar ƙasa irin su ɗaga tutar wata ƙasa, kira ga karɓe mulkin ƙasar ga sojoji da makamantansu, ya na mai cewa ba za su amince da hakan ba kuma za a hukunta duk wanda aka samu da aikata irin laifin kamar yadda doka ta tanadar.

Egbetokun ya kuma yi bayanin cewa ƴan sanda da sojoji ba su yi amfani da ƙarfin nuna isa ba kamar yadda aka zarge su. Ya ce, ƴan sanda sun yi ta ƙoƙarin tabbatar da masu zanga-zangar sun yi cikin aminci, illa amfani da borkonon tsohuwa da su kan yi a wasu lokuta la’akari da yanayi.

Bugu-da-ƙari, shugaban rundunar sojin ruwa, Emmanuel Ogalla ya tabbatar da ƴancin al’umma na yin zanga-zanga inda ya ce a wannan lokaci an samu yanayin da wasu ke ƙoƙarin tada zaune-tsaye, ya na mai cewa sun ƙwato ababe da dama a ɓangaren teku da albarkatun mai da ke ƙarƙashin kulawarsu.

Kazalika, shugabannin DSS da na shige-da-fice sun bayyana irin ƙoƙarin da su ke yi wajen ganin an daƙile ayyukan bata gari a sassa daban-daban na faɗin ƙasar.

Daga ƙarshe, sun yi kira ga kira ga al’ummar Nijeriya da su haɗe kansu wajen hana faruwar duk abin da zai tada tarzoma a cikinsu don zaman lafiya ya samu wanzuwa a ƙasar baki ɗaya.

By Babaji