Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga daga 8 zuwa 6 na yamma. Wannan ya biyo bayan majalisar tsaro ta jihar ta sake zama domin duba yadda abubuwa ke tafiya a cikin jihar.
Sanarwar ta fito daga Kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan a ranar 7 ga watan Agusta 2024.
Sanarwar ta bayyana cewa, mutane za su iya fitowa su cigaba da al’amuransu na rayuwa daga 8 zuwa 6 yamma.
In bamu manta ba, 4 ga watan Agusta gwamnatin Jihar kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon awa 24 a birnin kaduna da Zaria sakamakon zanga-zangar yunwa ta rikiɗe ta zama rikici wadda ta jawo asarar rai da dukiyoyi.
Majalisar tsaron ta shawarci mazauna garuruwan da su bada haɗin kai domin ganin an tabbatar da doka da oda.
