
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a biranen Jos da Ɓukuru.
Don haka, mazauna yankunan daga yanzu zasu ke zirga-zirga daga ƙarfe 2 na rana zuwa 6 na yamma.
Sanarwar ta fito ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan harkokin labarai na gwamna Caleb Murfwang.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan ya shawarci hukumomin tsaro da su ka yi tsayin daka wajen ganin an kiyaye dokar hana fitar a yankunan.
