Jigawa ta bai wa yara miliyan 1.4 rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta samu nasarar kammala bai wa yara ƙananan miliyan 1.4 magungunan rigakafin zazzaɓin Maleriya.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Jigawa, Dakta Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana haka, yayin da ya ke cewa an bai wa yara ‘yan ƙasa da shekara biyar maganin rigakafin zazzaɓin Maleriya na SMC, wato ‘Seasonal Maleria Chomopreɓention’ a faɗin jihar.

Ya ce an gudanar da wannan gagarimin aiki ne tare da Shirin Kawar da Zazzaɓin Maleriya na ‘Malaria Consortium Programme’.

Ya ce ƙananan yara 1,415,438 ne suka samu maganin na SMC a faɗin ƙananan hukumomi 27 da ke jihar.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin Daraktan Kula da Lafiya na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Mahmud Abdulwahab, ya ce yara waɗanda suka cancanci samun maganin su 1,446,533 ne a faɗin jihar. Kuma an samu nasarar isa ga yara 1,415,438, wanda hakan babbar nasara ce sosai da sosai.”

Ya ce za a yi aikin bayar da magungunan na rigakafin zazzaɓin maleriya har zagaye huɗu, waɗanda za a yi a cikin watannin Yuli, Agusta, Satumba da Oktoba.”

Sai dai kuma ya ce shirin raba gidan sauro da aka shirya farawa a ranar 9 ga Agusta, yanzu an ɗaga shi zuwa ranar 17 ga Agusta, 2024.

Ya ce halin zanga-zangar da aka shiga ne ya sa aka ɗaga ranar raba gidajen sauro ɗin, masu ɗauke da sinadarin maganin kashe sauro na ITN.

By ukarofi