Sojan gona: Ministar Mata ta sa an kama wacce ta shirya wani taro

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ministar harakokin mata, Uju Kennedy Ohanenye ta barrantar da kanta daga wani shiri mai suna ‘Unvieling the power of women and food security’ da aka yi ba da yawun ma’aikatar ba.

Ministar ta faɗi hakan ne a Abuja inda ta ce a halin yanzu an miƙa waɗanda su ka shirya shirin ga hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS kan zargin yin sojan gona ga ma’aikatar.

Ta ce, “a yau na samu sanarwar cewa akwai masu amfani da sunan wannan ma’aikatar wajen yin shirya wasu ayyukan da ba gaskiya be ne daga gare ta. Wanda a saboda haka ne na gudanar bincike kan lamarin da aka jingina wa ma’aikatar.”

Haka nan, ministar ta ce kamfanin wata mata mai suna Mela Chiyoma Pa Limited ke da alhakin yin hakan, ta na mai cewa ta miƙa ta hukumar DSS domin gudanar da bincike akan ta.

Ta kuma ce, “da ta shirya a madadin kanta, ta yi amfani da sunanta wajen yin gayyatar da kuma sanya sunanta ba sunan Ma’aikatar Harkokin Mata ba.

Bugu da ƙari, ta ce ba za ta bari a cigaba da shirin ba, saboda aiki ne na sojan gona kuma Mai Shugaban ƙasa bai ji daɗin hakan ba.

By Babaji