‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 64, sun kuma ƙwato kayan da ɓata-gari suka wawashe 

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta bayyana cewa ta kama matasa 64 da suka sace kayan jama’a da na gwamnati, ciki haɗa buhunan takin zamani 693 bayan da ɓatagarin suka ɓalle ma’ajiyar gwamnati, a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin tsaro da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.

Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiƙ Aliyu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a birnin Katsina.

Tun da farko rundunar ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga iyaye akan su kula da ‘ya’yansu tare da jan kunnensu akan su guji shiga ayyukan da suka saɓa wa doka waɗanda suka haɗa da shiga zanga-zangar tarzoma, ɓarnata kayan jama’a da kuma wawashe dukiyar gwamnati ko ta al’umma.

Sanarwar ta kuma ƙukaci matasan da su kasance masu kamun kai tare da ƙin yarda a yi amfani da su wajen tayar da tarzoma ko rikici.

A cewar kakakin rundunar, hukumar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro za su riƙa gudanar da sintiri akai akai domin tabbatar da bin dokar hana fita da aka sanya a faɗin jihar.

Daga ƙarshe rundunar ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da karya dokar za a hukunta shi.

By ukarofi