APC ta nemi a binciki jami’an gwamnatin Kano kan zargin karkatar da shinkafar tallafi ta Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta nemi a gudanar da bincike kan zargin sauya akalar shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta bai wa gwamnatin jihar a matsayin tallafi ga al’umma.

Shugaban Ma’aikata na gwamnan jihar, Shehu Sagagi ne ake zargi da karkatar da shinkafar.

Sai dai, Sagagi ya musanta zargin, ya na mai cewa shinkafar da aka samu a makarantar Islamiyyarsa shi ya saya da kuɗinsa yayin da wasu mutane suka bayar da taimakon wani ɓangare na shinkafar don ciyar da ɗalibai.

Amma shugaban APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce jam’iyyar ta damu da batun sauya akalar tallafin da ake samu da ƴan jam’iyyar NNPP ke yi a jihar.

Cikin wata sanarwa da Abbas ya fitar, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi bincike tare da bayyana masu hannu acikin ɓarnar, ya na mai gargaɗin cewa APC za ta kai ƙarar gwamnatin jihar matuƙar ta ƙi gudanar da binciken.

Abbas ya ce, an gano wasu ɗaruruwan buhunan shinkafa ɗauke da bajin da aka rubuta ‘Federal Government Food Security Program’ a makarantar Islamiyyar Wada Sagagi.

Sannan, Abbas ya ce a watan Disamban 2023 wani mai suna Tasi’u Al’amin Roba wanda ake zargi ya na yi wa sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Bichi aiki, an kama shi kan zargin karkatar da akalar kayan tallafin jihar.

“Gwamnatin ta na da ɗabi’ar sauya buhunan wasu daga cikin kayan hatsin da su ke son rabawa mambobinsu ɗauke da hoton gwamnan da bajin NNPP”, inji shi.

Hakan nan, a watan Satumban 2023 ne aka dakatar da Darakta Manaja na kamfanin raba kayan amfanin gona na jihar (KASCO), Dakta Tukur Ɗayyabu Minjibir kan sayar da kayan hatsin gwamnatin jihar ba bisa tsari ba.

Bugu da ƙari, ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ta aiko da tirela 70 na taki da nau’ukan ƙwayar hatsi da wasu ababe da za a raba wa manoma a kyauta, amma gwamnatin jihar ta yi kamar ita ta saya don a yabe ta. Ya kuma yi zargin an sayar da su ne akan Naira dubu biyar-biyar.

Kazalika, Abbas ya fassara ayyukan gwamnatin NNPP’n a matsayin hanyoyin daƙile ƙoƙarin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na tallafa wa al’umma a wannan lokaci na matsi.

By Babaji