
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Juma’a ne shugabar ma’aikatar ma’aikatu, Misis Folashade Esan ta gabatar da wacce za ta gaje ta a kujerarta, Misis Esther Wilson-Jack ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Esan ta ce Shugaba Tinubu ya yi sauyin yadda ya dace ganin yadda Wilson-Jack ta zauna da ita na tsawon makonni domin ɗaukar hannu daga gare ta, ta na mai bayar da tabbacin Esther za ta iya riƙe muƙamin yadda ake buƙata.
Ta kuma ce, sabuwar shugabar ta kasance mai ƙwazo, zaƙaƙura da kuma ƙwarewa ta salo daban-daban na gudanarwa.
Kazalika, Esan ta ce ba ta kokwanton cewa Esther za ta yi abin da ya dace domin hukumar ma’aikata ita ce reshen da za ta tabbatar da cika alƙawuran Tinubu ga ƴan Nijeriya.
A lokacin da ta ke jawabi, Esther ta ce ta yi godiya ga Shugaba Tinubu kasancewar ta wacce aka bai wa shugabancin ma’aikatar, ta mai cewa za ta iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ma’aikatar ta kai ga gaci.
