NIS ta gayyaci matar da ta yaga fasfo ɗin mijinta a filin jiragen sama na Legas

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar shige da fice, NIS ta na gudanar da bincike kan lalata wani fasfo ɗin Nijeriya da wata mata ta yi inda ta gayyace ta domin yin bayani kan haka.

Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa ya nuna yadda matar wacce matafiya ce ke ɗaiɗaita fasfo ɗin, wanda mallakin mijinta ne a filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Duk da cewa da farko ba a gano dalilin yin hakan ba, NIS ta ce aikin karya dokar ƙasa ce, kamar yadda mai magana da yawun NIS Kenneth Udo ya faɗa a ranar Litinin.

Udo ya ce, yayin da zargin da ake mata ya tabbata, za a hukunta ta kamar yadda doka ta tanadar, ya na mai cewa wajibi ne su kare martaba da kimar dokokin Nijeriya.

Haka nan, matar ta ce ta yi hakan saboda waɗansu dalilai na cikin gida inda ta ce ta na fuskantar matsaloli da dama acikin zaman aurenta wanda hakan ya sa ta ɗauki matakin abin da ta aikata.

Ta kuma bayar da haƙuri ga hukumar NIS kan faruwar al’amarin.

By Babaji