Yadda matasa suka binne ɗan uwansu da rai a Zariya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani lamari mai ban tsoro da ya faru a garin Zariya na Jihar Kaduna, wasu matasa biyu ’yan uwan juna sun binne ɗan uwansu mai suna Abubakar ɗan shekara 16 da rai sakamakon zarginsa da satar waya.

Batun da ya yaɗu a kafafen sada zumunta na yanar gizo da kuma tofin Allah-tsine, ya sa hukumomin jihar suka ɗauki matakin gaggawa, wanda ya sa aka kama matasan.

Hajiya Rabi Salisu, Kwamishiniyar Ayyukan Jinƙai da Cigaban Jama’a ta Jihar Kaduna, ta bayyana baƙin cikinta kan lamarin.

“Ban taɓa ganin an binne wani da rai ba ko a cikin fina-finai. Amma wannan yaron mai suna Abubakar ɗan shekara 16 ‘yan uwansa ne suka binne shi ne saboda zarginsa da satar waya,” inji ta.

Ta yi cikakken bayanin abin da ya faru mai ban tsoro, ta ce: “Sun haƙa rami, suka ɗaure hannunsa a bayansa, suka rufe bakinsa. Sun binne shi, kansa kawai ke waje, an lulluɓe shi da tsumma a cikin wani kango da ke kusa da wata gona. Wani matashi ne da ya ji yaron yana ihu jawo wasu manoma suka ceci yaron. An ɗauki wannan duka a cikin faifan bidiyo.”

Waɗanda ake zargin masu shekaru 22 da 18, ‘yan sanda sun kama su, kuma a halin yanzu suna fuskantar bincike.

Rabi Salisu ta jaddada ƙudirin gwamnati na kare haƙƙin yara da tabbatar da adalci.

“Ba za mu ɗauke shi da wasa ba. Kare haƙƙin yara da sauran waɗanda ake tauye wa haƙƙinsu a jihar Kaduna shi ne abu mafi muhimmanci a gare mu,” kamar yadda ta shaida wa manema labarai.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce waɗanda ake zargin suna tsare.

Ya bayyana cewa laifin ya samo asali ne daga zargin satar waya a Abuja, inda ’yan dukka uwan uku su ke aiki. Sun bi Abubakar suka koma shi har Zaria, inda suma binne shi da rai a matsayin wani nau’i na azabtarwa don hushe fushin satar musu waya. Hassan ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amince da aikata laifin.

Ma’aikatar kula da jin daɗin jama’a da cigaban jama’a ta jihar Kaduna ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah-wadai da lamarin tare da bayar da bayanai kan lamarin. 

Hajiya Rabi S. Ibrahim, Hon. Kwamishinar ga bayyana cewa: “Wanda abin ya shafa, Abubakar Aliyu, ya tsallake rijiya da baya, kuma tuni aka kuɓutar da shi. Waɗanda ake zargin dai sun haɗa da Yahaya Abdulkadir (20) da kuma Abdulkadir (17) ‘yan uwan ​​yaron, ‘yan sanda sun kama su.”

Jami’in jin daɗin jama’a na ma’aikatar da ke Zariya ya ziyarci al’umma domin duba halin da ake ciki tare da ba da tallafin da ya dace. 

Ma’aikatar ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci kuma za su ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin.

Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada ƙudirinta na kare haƙƙi da walwala ga ɗaukacin ’yan ƙasa, musamman ƙananan yara, kuma za ta yi ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

By ukarofi