
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kwamitin musamman kan satar ɗanyen mai na Majalisar Wakilai ya gargaɗi al’umma da babbar murya cewa ayyukan satar ɗanyen mai ya zo ƙarshe a ƙasar tare da alwashin duk wanda aka kama da hannu akan haka, to zai fuskanci hukuncin doka.
Shugaban kwamitin, Alhasan Ado Doguwa ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Juma’a.
Ya ce, ba za su bari gwamnatin shugaba Tinubu/APC ta cigaba da ciyo bashi daga ƙasashen waje ba sakamakon giɓi da ake samu a ɓangaren harkar mai da gas a Najeriya.
Ya kuma ce, ana samun ayyukan sace-sacen man ne ta hanyar rashin haƙurin matasa da kuma ɓarnata albarkatun ƙasa daga ɓarayi, ya na mai cewa lallai akwai buƙatar a dakatar da faruwarsu.
Doguwa ya ce, kwamitin na magana ne da umarnin Kakakin Majalisar, Hon. Tajuddeen Abbas musamman don gano haƙiƙanin dalilan da ke sabbaba koma baya harkar mai wanda jigo ne a tattalin arziƙin Najeriya.
Kazalika, wannan yunƙuri wani ɓangare ne na taimaka wa ƙoƙarin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta harkar tattalin arziƙin Najeriya domin sauƙaƙa wa al’umma al’amuransu na yau da kullum musamman a wannan lokaci na tsanani.
