Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya kawo rugujewar gidaje fiye da 250 a garin Natsinta da ke karamar hukumar Jibiya a Jihar Katsina.
Ruwan saman da ya ɗauki kusan kwanaki uku ana zabgawa a jihar ya kawo sanadiyyar faɗuwar gidaje ba a garin Natsinta ba ka ɗai harda wasu sassan jihar.
Ɗan majalisar dokokin mai wakilta karamar hukumar Jibiya Mustafa Yusuf ya nuna alhinin sa da jajantawa mutanen da suka rasa gidajen su.
Ɗan majalisar wanda ya ke magana a sa’ilin da ya kai ziyarar janjantawa ga al’ummar garin ya tabbatar masu da cewa majisar dokoki cikin gaggawa za ta ɗauki mataki a hukumance wajen ganin a tallafa masu.
Yayi kira ga masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar da su kawo ma al’ummar garin ɗauki na sutura da kayan abinci.
Wani mazauni garin Masa’udu Lawal ya shaidawa manema labarai cewa matsalar da ta kawo wannan bala’i shine na rashin magudanan ruwa inda yayi kira da ƙaramar hukumar Jibiya da ta ɗauki matakin gaggawa.
Yayi kira da masu hali da ‘yan kasuwa a ƙaramar hukumar da a kawo masu agajin gaggawa domin su sami natsuwa.
Haka ma a cikin garin Katsina gidaje da yawa suka ruguje a lokaci guda.
Lawal mai nama wanda abin ya shafa ya faɗa cewa makewayin sa da ɗaki guda sun ruguje sakamakon wannan mamakon ruwan.
Sai dai yace matsalar daɗewar gini ne, ga su kuma mafi yawan gidajen ƙasa ne su ke rugujewa.
Wata matsalar kuma da Lawal mai nama yace ya kawo wannan iftalai shine yadda mutane ke cike magudanan ruwan da shara hakan ya kawo toshewar hanyar fitar ruwa.
Yayi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta ƙaramar hukumar Katsina da su kawo ma su ɗaukin gaggawa domin su sake gyara muhallin su duba da halin matsin rayuwa da ba a taɓa fuskantaba a ƙasar.
