
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi ga manyan makarantu cewa za ta hukunta duk wadda ba ta miƙa jadawalin ɗaliban da ta bai wa gurbin karatu ba da wata uku bayan kammala bikin shiga.
An samu sanarwar ne daga hukumar jarrabawar shiga jami’a ta JAMB cikin wata takarda da ta fitar kamar yadda jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Fabian Benjamin, ya ce hakan ɗaya ne daga cikin matakan da kwamitin kawo ƙarshen takardun bogi a Nijeriya da gwamnatin tarayya ta naɗa ke ɗauka wajen ganin an tsaftace harkar ilimi a ƙasar.
Takardar ta ce, “A na buƙatar manyan makarantu su ke miƙa jadawalin ɗaliban da su ka ɗauka ga Ma’aikatar ilimi a cikin ƙasa da wata uku bayan kammala bukukuwan fara karatu ga sabbin ɗalibai.”
Kuma za a miƙa jadawalin ne ta hannun ofishin JAMB wanda zai tantance gabannin miƙawa ma’aikatar ilimi rahoton.
Hakan na zuwa ne bayan wani binciken bin diddigi da jaridar ‘Daily Nigerian’ ta yi na tona asirin masu amfani da takardun shedar kammala karatu na bogi daga Jamhuriyar Benin wanda a sanadiyyar haka gwamnatin shugaba Tinubu ta naɗa kwamitin bincike kan gano takardun bogi da dakatar da yaɗuwarsu A Nijeriya.
