
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar al’ummar Najeriya ƙarin kuɗin mallakar shaidar fasfo na fita ƙasashen waje.
Mai magana da yawun hukumar shige da fice (NIS), DCI Kenneth Udo ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matakin na zuwa ne yayin wani yunƙuri na inganta fasfo ɗin Najeriya.
A yayin kwaskwarimar da aka yi wa fasfo mai ɗauke da shafuka 32 wanda ke ƙarewa a wa’adin shekaru biyar da a ke sayar da shi a N35,000, daga yanzu, za a ke mallakar sa akan N50,000.
Sai wanda ke ɗauki da shafuka 64 da ke ƙarewa bayan shekaru goma wanda a ke sayarwa akan N70,000, daga yanzu za a ke sayar da shi akan N100,000 kachal.
Ya ce, sabon farashin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Satumba, 2024.
Kazalika, hukumar ta ce ta na mai bai wa waɗanda ke son mallakar fasfo ɗin haƙuri kan halin takura da hakan ka iya sanya su, yayin da ta yi mu su alƙawarin yin adalci da kuma isar da su cikin inganci ga masu buƙata.
