‘Yan sanda sun kama mutane 11 bisa zargin aikata fashi da makami a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar cafke mutane 11 da ake zargi da aikata fashi da makami a cikin garin Katsina.

Jami’in yaɗa labarai na hukumar ƴan sanda a jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da masu laifin inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin su, Isma’il Dawale ya jagoranci mutun biyar suka afka gidan Muntari Umar inda suka kwace masa Naira miliyan 1.85.

Bayan kwana biyu ne suka sake shiga gidan wasu mata a anguwar Filin Polo inda suka raba su da wayoyin hannu guda biyu da wasu ababe.

Haka kuma, jami’in ya kara da cewa sun samu nasarar kama ɗaya daga cikin masu fashin Keke-NAPEP, Ibrahim Umar ɗan shekara 26 wanda shi ma a unguwar Filin Polo a hanyar Katsina zuwa jibiya bayan ya saci Keke.

Sai Ahmadu Tijjani daga unguwar Jan Geɓe da ya sari ƙanin mahaifinsa.

ASP Sadiq ya kuma sanar da kama Halilu Yusuf na garin Shinkafi da yayi garkuwa da yaro mai suna Sulaiman Muntari ɗan shekara shida inda ya nemi a bashi Naira miliyan 6 amma jami’an ƴan sanda suka rutsa da shi.

By Babaji