
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Laraba ne aka tabbatar da rasuwar Sarkin Gobir, Isa Bawa wanda ƴan bindiga su ka yi garkuwa da shi bayan da aka gaza biyan kuɗin fansar da suka ce a kawo.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa, ƴan ta’addar ne suka kashe shi bayan ba a kai musu kuɗin da suka nema ba.
Da farko dai ba’a tabbatar da rasuwar Sarkin ba sai bayan zurfin bincike da aka gudanar wanda a sakamakon haka ne gidajen jaridu suka ta ruwaitowa ciki har da BBC inda al’ummar Gobir suka shiga alhini rashin.
Garkuwa da kuma kisan Sarkin sun haifar da ƙarin damuwa a yankin Arewa game da ayyukan ta’addanci da rashin tsaro wanda hakan ya ƙara sanya ƙoƙarin hukumomi na daƙile ayyukan ƴan ta’adda cikin babban ƙalubale.
Kawo yanzu dai babu wani jawabi daga hukumomi game da batun kisan Sarkin.
Al’ummar Gobir na cigaba da jimami da alhinin mutuwar Sarkin nasu yayin da ƙasa ta shiga ɗimuwa kan tasirin abin alhinin.
