Mun nuna wa ɗaliban GGSS Dukawuya yadda ake tafi da gwamnatin dimukraɗiyya – Hajiya Halima 

Spread the love

Daga MUHAMMMADU MUJITABA a Kano 

Hajiya Halima Ali Kabir, shugabar makarantar ‘yan mata ta Government Girls Secondary School Dukawuya Kano, ta bayyana farin cikinta kan yadda Malaman makarantar Dukawuya ke da ƙwazo wajen koyar da ɗalibansu dukkan darusan da ma’aikatar ilimin Kano ta tsara a koyar ɗaliban da tarbiyya mai kyau a Kano.

Hajiya Haiima ta bayyana haka ne a lokacin bikin yaye ɗaliban sama da 800 na GGSS Dukawuya, waɗanda suka kammala makaranta a wannan shekara ta 2024, wanda aka gabatar a harabar rmakarantar a ranar a Lahadin da ta gabata.                  

Har ilayau ta ce saboda ƙoƙarin malaman wannan makaranta da suka tsaya tsayin daka wajen koyar da ɗaliban muhimman abubuwa ciki har yadda ake tafi da gwamnatin dimukraɗiyyya cikin tsafta da tsarin sarautun gargajiya kamar yadda ake zaman majalisa da dai sauransu kamar yadda ɗaliban ke gudanar da wasan kwaikwayo a wannan taron.                                                                                                                          

A ƙarshe Hajiya Halima Ali Kabir ta yaba wa kwamishinan Ilimi na Kano Hon. Umar Haruna Dugawa, kan ƙoƙarinsa na bin umarnin Gwamna Abba Kabir Yusif wajen bunƙasa ilimin jihar da Hon Kabiru Ado Zakirai shugaban Hukumar kula malaman sakandare ta KSSSMB kan haɗin kai da yake ba makarutun Kano.

By ukarofi