Adalci da tausayi ne ke kawo zaman lafiya a ƙasa – Sarkin Malamai

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano        

An bayyana cewa bayan kasancewar mutum ya zama Musulmi babu wata ni’ima da tafi zaman lafiya muhimmanci a wanan duniya, domin ibada ko kasuwanci da komai ma ba zai yu ba sai da zaman lafiya.         

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Sheikh Kamilu Inuwa Musa, babban limamin masallacin Hidaya da ke Kundila Kano, a lokacin da yake fassarar huɗubarsa ta Juma’ar da ta gabata.            

Haka kuma ya ƙara da cewa shi kuwa zaman lafiya ba ya samuwa sai da tsayayyen Tauhidi wato kaɗaita Allah da bauta da imani da duk abun da ya yi umarni bawa ya yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta da sauransu.

“Haka kuma zaman lafiya na yaɗuwa idan aka samo shugabanci na adalai a kowane mataki na mulkin ƙasa wanann yana kawo zaman lafiya mara iyaka.  Amma a ce an samo shugaban ƙasa ko gwamna ko shugaban ƙaramar hukoma da sauran muƙamai ba adalai ba ƙasa ko al’umma ba zaman lafiya.

“Don haka duk wani shugaba tun daga kan mai gida da iyalansa sai ya ji tsoran Alllah ya yi adalci don samun zaman lafiya.    

“Tausayi ma jigo ne a zaman lafiya, domin tausayi daga mai ƙarfin arzuƙi ga talakawa raunana talakawa na kawo ƙauna tsakanin mawadaci da wanda ba shi da shi, don haka abun takaci ne mutom ya tara dukiya billiyoyi maƙotansa ko al’umma na kwana ko mutuwa da yunwa a ƙasa mai tarin albarka.”   

A ƙarshe Sarkin Malamai Sheikh Kamalu Inuwa Musa, ya yi nasiha ga ɗaukacin al’umma kan tsaya wa gaskiya, amana da neman sanin Allah da ƙoƙarin neman halal duk inda bawa ya samu kansa a rayuwa.

By ukarofi