Matasa ‘yan gida ɗaya sun rasu bayan mahaƙar ma’adanai ta rufe su a jihar Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu matasa biyu ‘yan gida ɗaya sun rasa rayukansu sakamakon ruftawa musu da ramin haƙar ma’adanai ya yi a ƙaramar hukumar Paikoro ta jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya.

Rahotonni sun ambato kakakin ma’aikatar ma’adanai ta Neja, Maureen Dibie, na cewa matasan – Zubairu mai shekara 20, da Sadiƙ mai 25 – sun gamu da ajalinsu ne lokacin da ramin ya rufta a kansu suna tsaka da neman zinare ranar Asabar da ta gabata.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kakaki makonni bayan wani ramin ya rufta da kusan mutum 50 a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Rahotonni sun ce ba a san da mutuwar matasan ba har sai da yamma ta yi kafin mahaifinsu Zubairu Ibrahim ya lura cewa ba su dawo gida ba domin cin abinci ko kuma sallar Magariba.

Kazalika, ba su sanar da iyayensu cewa za su je aikin haƙar gwal ɗin ba.

A cewar kakakin ma’aikatar, babban sakatare Yunusa Nahauni ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa ta’aziyya ga iyalansu.

By ukarofi