Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani labari na baya-bayan nan ya ci karo da kalaman da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ ya yi tun farko, inda ya yi iƙirarin cewa Majalisar ƙasa (NCS) ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da salon mulkin Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a yayin taron farko da ta yi a makon jiya.
Gwamna AbdulRazaƙ, wanda kuma ke riƙe da muƙamin Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), a baya ya bayyana cewa NCS da NGF tare sun nuna amincewarsu ga salon mulkin Shugaba Tinubu.
“Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron majalisar shi ne amincewa da salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya,” inji gwamnan Kwara.
Sai dai, wani babban jami’i da ya halarci taron ya musanta wannan ikirari, ya na mai bayyana shi a matsayin “labarin ƙarya da aka ƙirƙira a kafafen yaɗa labarai.”
Jami’in ya jaddada muhimmancin tarukan Majalisar Magabatan ƙasar, wanda ya samu halartar manyan mutabe da suka haɗa da tsaffin shugabannin ƙasa, da manyan jami’an shari’a da na majalisar dokoki.
Majiyar ta fayyace cewa, kai tsaye ba zai yiwu a bayyana ra’ayin irin wannan taro ba, tare da amincewa.
“Majalisar Magabatan babbar hukuma ce mai ba da shawara ga shugaban ƙasa. Ko kaɗan babu wani ƙudiri na muhawara ko amincewa a ajandarta,” inji jami’in.
A cewar majiyar, bayan kammala taron, babban lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayar da shawarar cewa, duba da yadda aka gudanar da zanga-zangar #EndBadGoɓernance, zai yi kyau majalisar ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Tinubu.
“Kusan nan da nan bayan shawarar AGF, Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio, ya tsaya tsayin daka, a cikin kalamansa, na biyu da buƙatar majalisar ta amince da salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” inji jami’in.
Sai dai ya ce babu wani tsohon shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, ko gwamnoni da suka halarci taron da ya yi tsokaci kan ƙudirin, wanda ke nuna rashin jin daɗin shawarar.
