Gwamnatin Nijeriya ta bayyana jami’o’in da ta amince da su a Togo da Benin

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami’o’i takwas ne kawai ta bai wa ’yan Nijeriya damar samun takardar shaidar digiri a ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ne ya bayyana haka a daren Lahadi yayin da yake magana a shirin Siyasa a gidan Talabijin na Channels a cikin makon nan.

Mamman, a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata don cika shekara guda a kan karagar mulki, ya bayyana cewa sama da ’yan Nijeriya 22,500 ne suka samu takardar shaidar digiri na bogi daga ƙasashen biyu, kuma za a soke irin waɗannan takardun a ƙasar.

Ministan ya ce, hakan na daga cikin rahoton da kwamitin da ke da alhakin binciken badaƙalar shaidar digiri na jami’o’in ƙasashen waje da na cikin gida a Nijeriya ya miƙa wa Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ya ƙara da cewa, wannan ci gaban ya biyo bayan rahoton binciken sirri da wani ɗan jarida ɗan Nijeriya ya samu digiri a wata jami’a a jamhuriyar Benin cikin ƙasa da watanni biyu ya kuma yi amfani da shi wajen shiga shirin yi wa ƙasa hidima.

Da yake jawabi yayin shirin, ministan ya ce gwamnatin tarayya ta amince da cibiyoyi uku ne kawai a Togo da biyar a jamhuriyar Benin, yayin da ta bayyana wasu a matsayin cibiyoyi da suka saɓa wa doka.

Mamman ya lissafta jami’o’in gwamnati a ƙasar Togo a matsayin cibiyoyin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da su wajen samun digiri ga ɗalibai daga Nijeriya kamar haka:

1. Jami’ar De Lome

2. Jami’ar De Kara

3. Jami’ar Katolika ta Afirka ta Yamma

Ministan ya kuma zayyana jami’o’i biyar da aka amince da su don ba da shirye-shiryen digiri a Jamhuriyar Benin ga ɗaliban Nijeriya kamar haka:

1. Jami’ar D’abomey-Calaɓi

2. Jami’ar De Parakou

3. Jami’ar Nationale Des Sciences, Ingenierie et Mathematiƙues

4. Jami’ar Nationale D’ Agriculture

5. Jami’ar Africaine De Deɓlopment Cooperatiɓe

Ministan ya kuma dage da cewa babu gudu babu ja da baya kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na soke satifiket kusan 22,700 da wasu jami’o’in ‘jagu’ da wasu jami’o’in ƙasar Togo da jamhuriyar Benin suka bai wa ’yan Nijeriya.

Mamman ya ci gaba da cewa matakin soke takardar shaidar bai yi tsauri ba saboda ‘yan Nijeriya da suka samu takardar shaidar digiri daga irin waɗannan manyan makarantun “ba bisa ƙa’ida ba” ya ɓata sunan ƙasar.

Ya ce, “Mafi yawan waɗanda ke gabatar da takardun shaidar bogi ba su ma bar gaɓar tekun Nijeriya ba, amma sun samu takardar shaidar ta hanyar cuwa-cuwa tare da haɗin gwiwar jami’an gwamnati a gida da waje.

“Jami’o’i na bogi” sun yi amfani da “hanzarin” ‘yan Nijeriya wajen ba su takardar jabu.

“Gwamnatin tarayya ta ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati da kuma sakataren gwamnatin tarayya za ta kamo waɗanda ke aikin gwamnati da irin wɗdannan takardun bogi. Ina kuma kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su yi koyi da shi.”

By ukarofi