Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai duba rikicin sayar wa matatun gida ɗanyen mai

Spread the love

Ƙaramin ministan man fetur na ƙasa, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti da zai duba rikicin siyar da ɗanyen mai ga matatar Ɗangote da sauran matatu na cikin gida.

Lokpobiri ya bayyana cewa kwamitin zai duba rashin jituwar da ke afkuwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar.

Ya umarci kwamitin wadda babban sakataren ma’aikatar ke jagoranta da su kawo rahoton binciken su daga nan zuwa ranar Litinin da Talata.

Ministan ya jaddada cewa dole ne masu ruwa da tsaki su tabbatar sun bi dokar mai PIA ta ƙasa da ta shafi siyar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida.

Idan bamu manta ba, a watan Yuli ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci kanfanin NNPC ya siyar da ɗanyen mai ga matatar Ɗangote da Naira.

Gwamnatin Tarayya ranar 15 ga Agusta ta kafa kwamitin da zai tabbatar da faruwan haka cikin hanzari ba tare da matsala ba.

Amma ministan Kuɗi Wale Edun ya tabbatar da cewa, sayar da ɗanyen mai ga Ɗangote zai fara ne ɗaya ga watan Oktoba.

By ukarofi