
Daga BELLO A. BABAJI
A cigaba da ƙoƙarin shawo kan matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Arewa-maso-Yammacin Nijeriya, ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya umarci shugaban Ma’aikatan Tsaro da wasu manyan jami’an tsaro su sauya sheƙa zuwa jihar Sakkwato.
Umarnin wani ɓangare ne na faɗaɗa ayyukansu don kawo ƙarshen ta’addanci da sace-sace da ke addabar yankin.
Ministan ya nuna damuwa sosai kan yadda ƴan ta’adda ke tada-zaune-tsaye musamman a jihohin Sakkwato, Zamfara, Katsina da Kebbi.
Ya ce, yayin kasancewar shugabannin tsaron a Sakkwato, za su mayar da hankali wajen ayyukan ƴan ta’addar musamman kan dakatar da ayyukan shahararren ɗan ta’adda, Bello Turji da masu aiki irin nasa.
Sakkwato ita ce hedikwatar da babban jami’in da zai jagoranci atsayen ya ke inda za su yi aiki a jihohi huɗu da aka lissafo a baya don dawo da zaman lafiya da tsaro a shiyyar.
A kwanan nan ne aka samu wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ga ƴan bindiga sun zagaye wata motar yaƙi ta sojoji su na murnar yin nasara.
Ganin haka ne ya sa Ministan ya yi watsi da al’amarin tare da cewa shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin taimaka wa jami’an a shirinsu na kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci.
