
Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanin Kula da filayen jiragen sama na Ƙasa (NAHCO Aviance) ya karrama wani ma’aikaci mai gaskiya, Auwal Ɗankode bayan da ya tsinci Dala dubu goma sannan kuma ya dawo da shi a lokacin da ya ke tsaftace wani jirgin sama a Kano.
Yayin da ya ke aikin nasa ne sai ya ga kuɗin wanda a bisa dukkan alamu mancewa aka yi da shi a kujera mai lamba ta 25H inda ba tare da ɓata lokaci ba ya miƙa wa shugaban tashar jirgin don a mayar wa mai shi.
Akan haka ne, NAHCO ta gayyaci Ɗankode zuwa hedikwatarta a filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas don haka ya bayyana godiyarsa game da karrama shi da aka yi.
Mista Indranil Gupta wanda shi ne Darakta-Manaja na NAHCO ya yaba wa Ɗankode kan ƙoƙarinsa da gaskiya da ya nuna yayin aikin nasa inda ya sanar da cewa za a ba shi kyautar kuɗi da kuma ƙara masa matsayi akan hakan.
Sannan baya ga haka, an naɗa shi matsayin sabon Ambasadan NAHCO.
Haka nan, an samu halartar manyan ma’aikatan kamfanin da kuma wasu daga cikin iyalan ma’aikacin a lokacin bikin karramawar.
