NNPC ya fara jigilar iskar gas zuwa Chana da Japan

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya fara jigilar iskar Gas zuwa Japan da Chana ta jirgin ruwa.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa, an cimma wannan buri ne ta hanyar haɗin gwiwar wasu rassan kamfanin wato NNPC LNG Ltd da NNPC Shipping Ltd.

Kamfanin NNPCL ya fara isar da iskar gas a ranar 27 ga Yuni, 2024 daga jirgin ruwa mai tsawon mita 174,000 Grazyna Gesicka a Futtsu, wani birni da ke Japan.

Bayan haka, kamfanin ya faɗaɗa ayyukansa zuwa ƙasar Chana, inda ya kai wani kaya na iskar gas ta jirgin ruwa.

Soneye ya bayyana cewa tsarin jigilar iskar gas ta jirgin ruwa na buaatar babban matakin ƙwarewa da inganci.

NNPCL yana kasuwancin iskar gas tun daga 2021, lokacin da ya fara sayar da iskar gas ɗin a karon farko a watan Nuwamba na shekarar 2023.

By ukarofi