Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin da zai binciko tashin gobara a gidan gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina ya kafa kwamitin da zai gaggauta bincikar dalilin tashin gobara a wani sashe na gidan gwamnatin jihar a Katsina.

Gobarar da ta tashi a sanyin safiyar Litinin, ta lalata ƙaramin ɗakin taro da ke kusa da ofishin Gwamnan jihar.

Sai dai jami’an kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jiha sun yi ƙokari wajen daƙile wutar kada ta bazu zuwa sassan gidan gwamnatin.

A cikin wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Yar’adua, daraktan yaɗa labaran ofishin sakataren gwamnatin jihar ya sanya wa hannu, ta ce an ɗora wa kwamitin alhakin gano dalilin tashin gobarar da irin ɓarnar da ta yi da sakacin da ya jawo tashin ta da kuma ba da shawarwarin yadda za a magance afkuwar hakan a gaba.

‘Ya’yan kwamitin sun haɗa da shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Katsina, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, kwamishinan kasafin kuɗi, kwamishinan shari’a, kwamishinan tsaron cikin gida da kwamishinan yaɗa labarai da sauransu.

By ukarofi