Matatar mai ta Ɗangote za ta fara siyar da mai ga gidajen mai na ƙasa.
Shugaban kamfanin Ɗangote, Alh Aliko Ɗangote ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Talata.
Ya cigaba da cewa fara bayar da man cikin gida zai rage yawan dogaro da man ƙasar waje da kuma rage dogaro da Dala.
Ya cigaba da cewa man da matatar ta shi za ta samar sai gogayya da kowanne iri a duniya wajen inganci da kyau.
Hakan zai gudana nan ba da jimawa ba da zarar kamfanin ya gama tattaunawa da kamfanin NNPC
