Shettima ya karɓi baƙuncin Ɗangote da Bill Gates a taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa

Spread the love

Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Aliko Dangote da Shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates na daga cikin waɗanda suka halarci taron majalisar tattalin arzikin Ƙasa (NEC) a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaban majalisar, Kashim Shettima ne ya jagoranci taron a cikin zauren majalisar. Kasancewarsu a taron bazai rasa nasaba da ƙoƙarin da gidauniyar su ke yi na kawo ƙarshen cutar Polio a Nijeriya ba.

Haka kuma a wajen taron akwai gwamnoni kamar su Babagana Zulum na Jihar Borno, Bala Mohammed na Bauchi, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Duoye Diri na Bayelsa, Francis Nwifuru na Ebonyi, Lawan Dauda na Jahar Zamfara, da sauransu. Taron yana faruwa kwana guda bayan ƙaruwar farashin fetur a faɗin ƙasar.

By ukarofi