Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Marigayiya Dada Musa ‘Yar’Adua, mata ce ga Marigayi Alhaji Musa Yar’adua, wanda ya riƙe sarautar Tafidan Katsina, kuma Mutawallen Katsina.
Musa ‘Yar’Adua shi ne tsohon Ministan Harkokin Legas (Minister of Lagos Affairs), kuma ɗan Majalissar Tarayya ne a Jamhuriya ta Farko, lokacin Gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa, daga 1960-1966.
Mai ƙimanin shekaru 102, mahaifiya ce ga Marigayi Janar Shehu Yar’adua, wanda shi ne mutum na biyu a Gwamnatin Soja ta Janar Olusegun Obasanjo.
Su Shehu ‘Yar’Adua ne suka miƙa mulki hannun farar hula, cikin 1979, ga Gwamnatin Shehu Shagari.
Shehu Yar’adua ya yi fice matuƙa a harkokin siyasar Nijeriya, wanda wannan ne ya sadaukar da rayuwar don ganin jamhuriya ta huɗu da muke ciki ta siyasa ta ɗore, kuma ta zauna daram da gindinta.
Dada ita ce mahaifiyar tsohon Shugaban ƙasa, Umaru Musa ‘Yar’Adua, wanda ya yi Gwamnan Jihar Katsina tsawon shekaru 8, sannan ya yi shugaban ƙasa tsawon shekara biyu da rabi, kafin rasuwarsa.
‘Ya’yan Dada biyu sun yi takarar shugabancin Najeriya a lokuta daban-daban. Shehu bai samu nasara, Umaru kuma ya yi nasara a 2007.
Dada ce matar da ɗan ta Umaru, shi ne ya fara rasuwa ya na kan mulki a tsarin dimokraɗiyya a Jamhuriyar Najeriya. Kuma mutuwar ta ciwon ajali, ba ta hanyar kisan juyin mulki ba.
Ita ce mahaifiyar Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, wanda a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. Kuma Kanar ne na soja kafin ya yi ritaya, sannan ya shiga siyasa.
Kaka ce ga Murtala Yar’Adua Tsohon ƙaramin Ministan Tsaro a lokacin Gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan.
Tsofaffin Gwamnonin Katsina, Bauchi da Kebbi na daga cikin mutanen da ke auren jikokinta, wanda tsohon Shugaban ƙasa Umaru ne ya haifi jikokin uku.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya jajenta wa iyalan ‘Yar’adua bisa rasuwar Hajiya Dada a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce Shugaba Tinubu yana miƙa ta’aziyyarsa ga Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, al’ummar Jihar Katsina, da sauran jama’ar da rasuwar marigayiyar ta shafa.
Shugaban da yake sake jajenta rasuwar Hajiya Dada, ya yaba halayenta na gari da suka haɗa da tausayi da imani da gaskiya da zumunci.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayiyar tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da tunawa da ita bisa goyon baya da zaman lafiya da gudunmawarta ga ƙasa.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana Marigayiya Dada a matsayin uwa ga
Raɗɗa ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai a gidansa da ke gidan gwamnati.
Ya ƙara da cewa Allah ya albarkaceta da ‘ya’ya da suka riƙe shugabancin Nijeriya wanda haka bai sa ta canza mu’amullanta da al’umma ba.
Gwamnan ya bayyana cewa a kodayaushe cikin hidimar taimakawa mabuƙata take kamar yadda duk mai wucewa ƙofar gidanta ya gani.
”Allah ya albarkaceta da ‘ya’ya kamar su Marigayi Shehu Musa Yar’adua da ya riƙe muƙamin babban hafsan hafsoshi Nijeriya da Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua da ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa da Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da yanzu sanata ne,” Dikko Raɗɗa ya ce.
Ya cigaba da cewa wannan babbar baiwa ce da Allah ya yi mata amma ba ta canza fuska ba wajen tausaya wa al’umma.
Gwamnan ya yi fatan Allah karɓi shahadarta, ya kai rahama ga kabarinta.
Ya kuma miƙa godiyarsa da wakilin shugaban ƙasa Kashim Shetima da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar da gwamnoni da ‘yan majilisar ƙasa da sauran manyan mutane da suka halarci jana’izar marigayiyar.
Hakazalika Majalisar Dattawan Nijeriya ƙarƙashin mataimakin majalisar Sanata Barau Jibrin, ya jagoranci ziyarar ta’aziya na rasuwar Hajiya Fatima Dada a Katsina.
Sanata Barau Jibrin ya yi addu’a Allah yafe mata kura-kuranta ya albarkaci abinda ta bari.
Ya kuma shawarci Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da ya ɗauki mutuwarta a matsayinsa na Musulmi da babu wanda zai wuce lokacinsa.
Ya bayyana Marigayiya Dada a matsayin mace mai taimakon al’umma inda a kullum akwai dandazon mabuƙata da take taimaka masu da maƙota suka shaida.
A cikin waɗanda suka rufa masa baya akwai Sanata Abdulhamid Musa shugaban kwamitin harkokin ‘yan sanda da Sanata Aminu Iya Abba mai kula da kwamitin Kimiyya da Fasaha.
Akwai kuma Sanata Muntari ɗandutse mai wakiltar shiyar Funtuwa a jihar Katsina.
