Ƙungiyar ‘Yan Gwan-gwan ta NASWEDN ta sha alwashin tsaftace sana’arsu              

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Ƙungiyar ‘Yan Gwan-gwan ta ƙasa reshan Jihar Kano NASWDEN, ƙaƙarshin shugabanta na Arewa Alhaji Aminu Lawan Soja, ta yi alƙawarin kawar da ɓata-gari a sana’arsu kamar dai yadda sabon shugaban kwamitin kar-ta-kwana kuma sakataren ƙunƙiyar na Jihar Kano, Kwamared Idiris Adamu Gaya ya bayyana a madadin shugaban ƙungiyar na Arewa, Aminu Hassan Soja wurin taron ƙasa da NASWDEN da ta gabatar a ranar Laraba a birnin Kano.                

Adamu Gaya ya nemi kyakkyawan haɗin kan ‘yan ƙungiyar wajen bin doka da oda domin gyara sunan sana’arsu da wasu ke son ɓatawa suna a ƙasar nan. Don haka ya ce za su haɗa kai da ‘yan jarida da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na yin aiki ba sani ba sabo, ga duk wani mai ƙoƙarin ɓata sunan ƙungiyar da karya dokokinta.        

Shi ma Alhaji Sunusi Bashir, Ma’ajin ƙungiyar ta NASWED reshen jihar Kano, ya ce harkar man fetur ce kawai ta fisu fitar da kaya ƙasashen ƙetare bayan sun sayar a gida Nijeriy, saboda kanyan da su ke samar wa ya fi ƙarfin kamfanonin Nijeriya su sarrafasu wanda kuma sana’ar ta samar da aiki ga jama’ar Kano sama da milliyon biyu da kuma milliyoyin mutane a faɗin Nijiriya.”

By ukarofi