Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya caccaki kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPCL, bisa rashin gaskiyar da ya yi biyo bayan karɓar bashin dala biliyan 6 daga dillalan man fetur.
Atiku ya ce, wannan lamari ya ƙara tsananta ƙarancin man fetur da ya addabi al’ummar ƙasar tsawon makonni shida.
Babban jami’in sadarwa na kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da biyan bashin, inda ya bayyana irin matsanancin halin ƙuncin da ya saka ayyukan kamfanin.
“NNPC ya amince da rahotannin baya-bayan nan game da ɗimbin bashin da yake bin masu samar da mai. Wannan matsalar kuɗi na barazana ga ɗorewar samar da mai,” inji Soneye.
Ya ba da tabbacin cewa NNPC ya ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikinsa na samar da mafita ta dindindin, kamar yadda dokar masana’antar man fetur ta PIA ta bayyana, kuma tana aiki tare da hukumomin gwamnati don tabbatar da samar da albarkatun mai a faɗin ƙasar nan.
Yayin da ya ke mayar da martani kan wannan lamari, Atiku ya bayyana matuƙar damuwarsa kan lamarin ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu.
Ya kuma zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ruguza kamfanin na NNPC, inda ya kwatanta ayyukan da a ke yi a halin yanzu a matsayin “ƙoƙarin rusa kadarorin Nijeriya.
