Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta musanta cewa cewa ‘yan bindiga sun ƙwace motoci masu sulke guda biyu na sojoji a Jihar Zamfara.
Ta ce, kuma musanta iƙirarin cewa an hallaka mutane masu yawa waɗanda ’yan ta’adda suka binne tare da rahotannin sace mutum 150 a Sokoto.
Martanin na hedikwatar na zuwa ne bayan wasu bidiyoyi sun yaɗu wanda suke nuna ’yan bindiga na murnar ƙwace motocin sojojin.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, daraktan yaɗa labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana bidiyoyin a matsayin na ƙarya.
Da yake bayani kan abin da ya faru a Zamfara, Edward Buba ya bayyana cewa motocin sun maƙale ne a cikin taɓo yayin da suke ƙoarin farmakar ‘yan bindigan a ƙauyen Kwashabawa.
Ya ƙara da cewa, dakarun sojojin sun cire kayayykin da ke da amfani a cikin motocin domin hana ‘yan bindigan yin amfani da su.
Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa bidiyon da aka yaɗa wanda ya nuna ’yan ta’adda na binne mutane masu yawa ba a ƙasar nan ya faru ba.
Ya bayyana cewa jita-jitar da aka yaɗa kan cewa an sace mutane 150 a Sokoto, an yaɗa ta ne domin a dusashe nasarar da sojoji suke samu kan ’yan ta’adda.
