Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya soke kwangilar gina titin mai tsawon kilomita biyar a ƙaramar Hukumar Garko, saboda zargin gazawar ɗan kwangilar da bai wa aikin gina titin.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na gwamna Sanusi Tofa ya fitar a Kano, kuma ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Tofa ya ce, gwamnan ya tabbatar wa al’ummar ƙaramar hukumar cewa za a naɗa sabon ɗan kwangila mai inganci nan da ‘yan kwanaki masu zuwa domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.
“Gwamnan ya kuma bayyana ƙudurinsa na kafa cibiyar lafiya ta zamani a Garin Garko, da nufin kusantar da harkokin kiwon lafiya ga jama’a.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ya nuna godiya ga ci gaba da goyon bayan da al’ummar yankin ke bayarwa, ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa wajen samar da ci gaba.”
Haka kuma gwamnan ya gudanar da aikin tantance aikin noman danina na Kafinchiri a yankin.
“Ya ce shirin yana ƙarƙashin shirin kawo sauyin noma a jihar. Ya bayyana cewa, aikin wanda aka kiyasta kuɗinsa ya kai Naira biliyan 2.5, an yi shi ne domin bunƙasa noma a duk shekara, da inganta samar da abinci da kuma bunƙasar tattalin arzikin jihar,” inji shi.
Tofa ya ci gaba da cewa, “Ya jaddada muhimmancin aikin, yana mai cewa wani muhimmin ɓangare ne na ƙoaarin gwamnatinsa na bunƙasa noman noma a jihar.”
Ya kuma ƙara da cewa, gwamnan ya buƙaci mazauna garin Garko da kewaye da su yi amfani da damar da aikin ya bayar don inganta zamantakewa da tattalin arzikin su da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban jihar baki ɗaya.
