Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hedimastan makarantar firamare ta Gaidar Makada da ke Jihar Kano ya shiga hannu kan sayar da kujeru da wasu kayayyakin makarantar ta bayan fage.
Hukumar Karɓar ƙorafi da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano ce ta kama hedimastan makarantar da ke yankin ƙaramar Hukumar Kumbotso kan zargin wannan badaƙalar.
Mai magana da yawun hukumar, Kabir Abba Kabir, ya ce an kama hedimastan ne bayan da aka gano wani shirin sayar da kayan makarantar ta ƙarƙashin ƙasa.
Kabir ya sanar a ranar Asabar cewa a sakamakon haka ne hukumar ta gudanar da bincike kan lamarin kuma tana ƙoƙarin ƙwato kayan makarantar da hedimastan ya sayar.
A cewar jami’in, “bincike ya gano wasu muhimman kayan makarantar da aka sayar, irin su ƙarafa da kujeru da bencina da sauransu, waɗanda suka yi layar zana a makarantar.
“Hedimastan makarantar ne ake zargi sakamkon ƙumbiya-ƙumbiya da aka gano aka kuma gabatar a lokacin zaman hukumar kula da makarantu da kuma shugabannin ƙungiyar iyaye da malamai.
“A yau (31 ga watan Agusta, 2024) aka kawo mana ƙara a hukumace, mu kuma nan take muka ɗauki mataki.
“Hukumarmu ta duƙufa wajen ƙwato kayan daga hannun waɗanda suka saye su, da kuma tabbatar da tsaftace ɓangaren ilimin jihar Kano nan daga ayyukan bara-gurbi.”
