Daga GAMBO ISA
Shugabar ƙaramar Hukumar Jere ta jihar Borno, Hajiya Inna Galadima, ta yaba wa gwamnan jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, kan ci gaban da yake samarwa a jihar.
Da take magana a wata hira da manema labarai, ta zayyana wasu nasarorin da gwamnan ya samu a fannin raya walwalar ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa da dai sauransu.
Hajiya Galadima ta zayyano wasu nasarori da suka haɗa da: Bunƙasa ababen more rayuwa da tsare-tsare na jama’a kamar gina gidaje, samar da manyan motoci da tituna a ƙaramar hukumar Jere da kuma cikin ƙananan hukumomi 27 da babban birnin jihar da samar da gadar sama a Maiduguri babban birnin jihar.
A yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya, ya ce gwamna ya sayo kayayyaki ga jami’an tsaro da hukumar tsaro ta CJTF domin yaƙar ta’addancin Boko Haram a jihar.
Ta ce gwamnan ya kuma taɓa ɓangaren marasa galihu a Jere da sauran ƙananan hukumomin jihar.
Hajiya Galadima ta shawarci matasa da su kasance jakadun yankin a kodayaushe.
Ta buƙaci matasa su yi biyayya ga dokokin tsarin mulki, su guji miyagun ƙwayoyi da mutunta dattawa.
Ta ce salon shugabanci na hangen nesa na gwamna ya zo daidai da gidauniyar da mataimakin shugaban ƙasa na yanzu Sanata Kassim Shettima ya kafa.
Ta shawarci shugabannin ƙananan hukumomi 27 da aka zaɓa waɗanda za su fara aiwatar da shirye-shirye na Zulum kuma su kasance masu amana ga jama’arsu yayin da masu zaɓe ke fatan samun ribar dimukuraɗiyya.
