Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A wani gagarumin yunƙuri na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar Arewacin Nijeriya, Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jaddada damuwar hadin kan gwamnonin yankin na magance matsalar.
Gwamna Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar cikakken rahoto daga gamayyar ƙungiyoyin Arewa CNG, wanda kwamitin ƙwararru kan rashin tsaro a arewacin Nijeriya ya shirya.
Rahoton dai na ɗaya daga cikin muhimman sakamakon taron da aka kammala kwanan nan a Abuja, da nufin samar da mafita mai ɗorewa kan ƙalubalen tsaro a yankin.
Gwamna Yahaya ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda rashin tsaro ke yi ga rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya, musamman a fannin noma, wanda ya taɓarɓare sosai.
Ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kayan abinci ba jahohin Arewa kaɗai ya shafi al’ummar ƙasa baki ɗaya.
“A matsayinmu na gwamnoni, mun damu matuƙa game da matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.
“Wannan yanki yana da kaso mafi yawa na al’ummar ƙasar kuma yana da albarkatun ma’adinai da kasa mai albarka da ta dace da noma. ƙarfin aikin gona na yankin na taka rawar gani wajen tabbatar da wadatar abinci a Nijeriya.
“Abin takaici, rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu yana kawo cikas ga waɗannan ayyuka, yana haifar da tsadar kayan masarufi, wanda ya shafi dukkan ‘yan Nijeriya, ba wai kawai na Arewa ba,” in ji Yahaya.
A ƙarƙashin jagorancinsa, NSGF na shirin gudanar da wani taro mai zurfi wanda zai haɗa dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanni na da da na yanzu, da sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, da ƙungiyoyin fararen hula. Manufar ita ce tattaunawa da aiwatar da dabarun da za su dawo da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzikin yankin.
“A wannan karon, muna son ɗaukar matakin haɗin gwiwa kan batun rashin tsaro. Wannan rahoto ya dace. Za mu yi nazari tare da aiki tare don aiwatar da shi.
“A halin yanzu muna shirin gudanar da wani taro mai zurfi tare da dukkanin masu ruwa da tsaki a yankin don kara nazarin yadda za mu haɗa kai don samar da hanyoyin da za su magance waɗannan matsalolin gaba ɗaya,” in ji gwamnan.
Shugaban tawagar CNG, Bashir Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa rahoton da aka gabatar ya samo asali ne sakamakon dogon aiki da aka yi, wanda ya yi nazari kan yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a Arewacin Nijeriya da nufin samar da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar.
Rahoton ya haɗa da tsarin dukkanin al’umma, wanda ƙungiyar ta ɓullo da shi, da nufin samar da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a faɗin yankin wajen magance matsalar rashin tsaro.
